Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun sako sauran fasinjojin jirgin Kaduna-Abuja

An sako dukkan fasinjojin jirgin kasan nan da aka sace daga akan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abujan Najeriya, ranar 28 ga Maris, 2022, a cewar gwamnatin kasar.

Harin jirgin kasa kan hanyar Abuja-Kaduna
Harin jirgin kasa kan hanyar Abuja-Kaduna © AP
Talla

Farfesa Usman Yusuf, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron kwamitin da ke bibiyar lamarin ne ya bayyana hakan a yammacin Larabar nan.

“Al’ummar kasa na mika godiya ga Sojojin Najeriya karkashin jagorancin wannan kwamiti wadanda suka jagoranci wannan aiki tun daga farko har karshe. Dukkan Hukumomin Tsaro da Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya sun ba da gudunmawa sosai ga wannan aiki,” in ji Farfesa Yusuf.

Yace tallafin da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ke bayarwa shi ne ya taimakawa wajen samun mafitar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.