Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kone ofishin 'yan sanda a Enugu

‘Yan bindiga sun kai hari tare da cinna wuta kan babban ofishin ‘yan sanda da ke yankin Inyi a karamar hukumar Udi a jihar Enugu.

Misali na 'yan bindiga.
Misali na 'yan bindiga. © Daily Trust
Talla

Harin ya kai ga mutuwar dan sanda da wani farar hula wanda aka ce ya je ofishin ne domin shigar da kara.

Wani ganau ya ce maharan su shida ne kuma sun zo ne cikin motoci biyu, inda bayan shafe mintuna da dama suna harbe-harbe, sunka cinna wuta kan ginin hedikwatar ‘yan sandan da ya kasance bene mai hawa daya.

Enugu dai na daga cikin jihohin yankin kudu maso gabashin Najeriya da sukai fama da hare-haren ‘yan bindigar haramtacciyar kungiyar IPOB, musamman a watannin baya, inda maharan suka rika afkawa jami’an tsaron da suka hada da sojoji da ‘yan sanda a shingayen bincike, da kuma ofisoshin ‘yan sanda.

A cikin watan Mayun da ya gabata, gwamnan jihar Anambra Charles Chukwuma Soludo ya ce akasarin ‘yan bindigar da ke kai munanan hare hare suna kashe mutane a jihar sa ‘yan kabilar Igbo ne, sabanin zargin da wasu mutane ke yi cewa baki ne daga wasu sassan kasar.

Soludob ya bayyana haka ne a waccan lokaci, a yayin da yake kafa dokar hana fita ta sa’oi 24 a wasu kananan hukumomin jihar guda 7 da ake fama da hare-haren ‘yan bindigar haramtacciyar kungiyar IPOB.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.