Isa ga babban shafi

Najeriya: Kotun daukaka kara ta sallami Nnamdi Kanu daga zargin cin amanar kasa

Kotun daukaka kara a Najeriya ta wanke shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu daga tuhumar da gwamnatin kasar ke masa na laifuffuka guda 7 da suka shafi ayyukan ta’addanci da kuma cin amanar kasa.

Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu.
Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu. STRINGER / AFP
Talla

Mai shari’a Jummai Hannatu ta jagoranci tawagar alkalai guda 3 wajen soke karar da lauyoyin gwamnatin Najeriya suka gabatar a gaban kotun.

Hannatu tace kotun bata da hurumin sauraron karar da aka gabatar mata bayan tasa keyar Kanu daga kasar Kenya zuwa Najeriya sakamakon tsallake belin da aka bashi.

Gwamnatin Najeriya na zargin Kanu da jagorancin haramcaciyar kungiyar IPOB wadda ‘yayan ta ke kai munanan hare haren ta’addanci akan jami’an tsaro da kuma mutanen dake adawa da manufarsu ta kafa kasar Biafra.

Gwamnatin tace Kanu na amfani da tashar rediyon sa wajen tinzira jama’a suyi bore da kuma aikata laifuffukan cin amanar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.