Isa ga babban shafi

Buhari zai yi balaguro zuwa Koriya ta Kudu

Shugban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Koriya ta Kudu ranar Lahadi domin halartar wani taron harkokin lafiya na duniya mai taken World Bio Summit, 2022.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin shirin balaguro zuwa birnin London a Birtaniya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin shirin balaguro zuwa birnin London a Birtaniya. © Presidency / Sunday Aghaeze
Talla

Taron wanda Koriya ta Kudu tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya suka shirya, na kwanaki biyu zai gudana tsakanin ranakun 25 zuwa 26 ga watan Oktoba.

Taken taron dai shi ne 'Makomar Rigakafi da Lafiya'

Sanarwar da Fadar Shugabancin kasar ta fitar ranar Asabar, ta ce Najeriya tare da wasu kasashen Afirka biyar ne za su halarci taron, wanda za a ba da horo kan yadda za a dinga samar da rigakafin cutuka bisa fasahar mRNA ga nahiyar Afirka.

Daga cikin wadanda za su yiwa shugaba Buhari rakiya zuwa Koriya ta Kudu, akwai ministan lafiya Osagie Ehanire, shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye da shugaban hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta NCDC, Dakta Ifedayo Adetifa.

Sauran sun hada da wasu gwamnoni, ministoci da kuma wasu manyan mukarraban gwamnati.

Sanarwar fadar shugabancin kasar ta ce, ana sa ran shugaba Buhari zai koma gida da zarar an kammala taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.