Isa ga babban shafi

Kasashen yamma sun yi gargadi kan barazanar kai hari Abujan Najeriya

Ofishin jakadancin Amurka ya fitar da sanarwar tsaro kan karuwar hare-haren ta'addanci a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

President Muhammadu Buhari of Nigeria
President Muhammadu Buhari of Nigeria © Nigeria presidency
Talla

Bayan gargadin ta'addanci na Ofishin Jakadancin Amurka, hakama na Biritaniya ya shawarcin ‘yan kasar mazauna Najeriya, da su yi taka tsan-tsan.

A cewar rahotanni, sauran kasashen Turai, na gargadin jama’arsu mazauna Najeriya da su takaita zirga-zirga, said ai idan bukatar dole ta taso.

A cikin martanin da ta mayar, hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi kira da a kwantar da hankula, inda ta ce ana daukar matakan da suka dace don tabbatar da tsaro a babban birnin tarayya Abuja da sauran sassan Najeriya.

A cewar wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar, za a iya kai harin ta’addancin a gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni, manyan kantuna, otal-otal, mashaya, gidajen cin abinci, wuraren wasannin motsa jiki, tashoshin sufuri, wuraren tabbatar da doka da kuma kungiyoyin kasa da kasa. 

Wannan sanarwar ta baya-bayan nan ta biyo bayan rahoton leken asirin da aka fitar a watan Satumba na yiwuwar kai hare-hare a cibiyoyin soji a Najeriya. Daya daga cikin wadanda aka kai harin dai ita ce Makarantar horas da Sojojin Najeriya, da ke Kachia, wadda ke dauke da manyan makamai na biyu mafi girma a kasar, bayan wadda ke Ikeja.

Rahoton ya ce 'yan ta'addar sun shirya kai manyan hare-hare a wurare dabdan-daban da ke birnin tarayya Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.