Isa ga babban shafi

Kungiyar kwadago ta NLC ta yi watsi da tsarin gwamnati na ‘‘ba aiki ba biya’’

Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta yi watsi da tsarin gwamnati na ''ba aiki ba biya'' da kasar ke son yin amfani da shi kan Malaman jami’o’I da suka shafe watanni 8 suna yajin aiki wadanda a baya-bayan nan suka janye tare da komawa bakin aiki.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta kasa NLC, Ayuba Wabba.
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta kasa NLC, Ayuba Wabba. © The Guardian Nigeria
Talla

NLC ta bukaci gwamnati ta cika dukkanin alkawuran da ta kulla da kungiyar ta ASUU gabanin komawa yajin aikin, ciki kuwa har da abin da ya shafi hakkokinsu na albashi da kuma kyautata aikinsu.

Cikin wata takaddar bayan taro da kwamitin kolin kungiyar ya bayar bayan ganawarsu a jihar Kebbi dauke da sa hannun Ayuba Wabba ta bayyana cewa wajibi gwamnatin kasar ta saki dukkanin hakkin malaman na kungiyar ASUU a tsawon lokacin da suka dauka suna yajin aikin.

An shafe tsawon watanni 8 ana kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar ASUU dangane da yajin aikin gabanin cimma jituwa a makon jiya, wanda ya bayar da damar janye yajin aiki.

Sai dai Ministan kwadago na Najeriyar Chris Ngige ya ce har sai kotu ta kammala shari’ar da ke gabanta game da yajin aikin na ASUU ne tukuna za sus amu tabbacin yiwuwar biyan malaman ko akasin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.