Isa ga babban shafi

Kada ku razana da sanarwar Amurka da Birtaniya - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci jama’ar kasar da su kwantar da hankulansu sakamakon gargadin da ofisoshin Jakadancin Amurka da Birtaniya suka gabatar na yuwuwar kai harin ta’addanci a birnin Abuja.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © rfi
Talla

Buhari wanda ya koma Najeriya yau bayan tafiyar da yayi zuwa kasar Koriya ta Kudu, ya bukaci hukumomin tsaron kasar da sauran jama’a da su sanya ido akan abubuwan dake faruwa kusa da su domin kare lafiyarsu.

Shugaban wanda yace sanarwar da gwamnatocin kasashen suka gabatar ba wai ya tabbatar da kai hari a birnin Abuja bane, saboda haka ya dace mutane su kwantar da hankalinsu domin kuwa jami’an tsaro sun tsaurara matakan da suke dauka tun bayan harin gidan yarin Kuje a watan Yuli.

Sanarwar da mai magana da yawunsa Garba Shehu, ya rabawa manema labarai tace Najeriya bata banbanta da wasu kasashen duniya da ake gabatar da irin wannan gargadi akansu ba, kuma Amurka da Birtaniya sun bada irin wadannan sanarwar akan wasu kasashen yammacin duniya dangane da abinda ya shafi barazanar kai harin ta’addancin.

Buhari yace jami’an tsaron Najeriya na taka rawa sosai wajen dakile shirin kai irin wadannan hare hare da dama da kuma zakulo masu kitsasu domin kare lafiyar jama’ar kasa, yayin da ya kara da cewar tsaron rayuka da dukiyar 'yan Najeriya zai ci gaba da zama mai muhimmanci a karkashin gwamnatinsa.

Shugaban wanda ya jinjinawa sojojin kasar da sauran hukumomin tsaro, ya kuma bukaci kara kaimi domin tabbatar da zaman lafiya yayin da ake tunkarar karshen shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.