Isa ga babban shafi

Buhari zai kaddamar da aikin hako mai na farko a Arewacin Najeriya

A ranar Talata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara arewacin kasar domin duba aikin hako mai na farko a rijiyoyin mai dake jihohin Bauchi da Gombe.

Wannan shine karon farko da za a kaddamar da wani shirin hako danyen mai a Arewacin Najeriya.
Wannan shine karon farko da za a kaddamar da wani shirin hako danyen mai a Arewacin Najeriya. © premium times
Talla

Bikin kaddamar da aikin hako man na Kolmani mai lamba 809 da 810 a filin Kolmani zai kasance aikin hako mai na farko a Arewacin Najeriya.

An gano man a yankin arewacin kasar ne kimanin shekaru biyu da suka wuce.

Yayin da Najeriya ta dade da fara hako danyen mai a kudancin Neja-Delta, wannan bincike da aka yi a arewacin kasar zai kasance na farko bayan dakile wani yunkurin da aka yi a yankin Borno sakamakon rashin tsaro.

Tun a shekarar 2016 ne, Kamfanin NNPC ya kaddamar da aikin neman mai a wasu jihohin Arewa wanda ya kai ga gano man a jihohin Bauchi, Gombe, Borno da kuma Neja.

A cewar kamfanin NNPC, kamfanin mai na Sterling Global Oil da hukumar samar da gaban Najeriya NNDC da kuma kamfanin NNPC ne za su samar da rijiyar mai a yankin Bauchi da Gombe.

"Za a yi bikin kaddamar da aikin ne a ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba kuma zai samu halartar shugaban kasa da kansa tare da mafi yawan 'yan majalisar ministocinsa ciki har da karamin ministan mai, Timipre Sylva.

Bisa sabuwar dokar kula da bangaren albarkatun man fetur ta 2022, kudaden da ake kashewa wajen hako man fetur ya karu zuwa kashi 30 cikin 100, wanda hakan ke nufin kamfanin mai na NNPC zai samu karin kudade don bunkasa rijiyoyin mai a Najeriya.

A halin yanzu, Hukumar kula da albarkatun man tetur ta Najeriya ta ce akwai danyen mai da ya kai ganga biliyan 37 a rumbun adana danyen mai na Najeriyar.

Rahotanni sun ce rijiyoyin na Kolmani zai iya adana sama da danyen mai biliyan daya, wanda kuma hakan zai iya habaka arzikin man Najeriya daga nan zuwa shekaru 10 masu zuwa.

Gano man fetur a arewacin kasar na zuwa ne a daidai lokacin da yawan danyen mai da ake hakowa a kudancin kasar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.2 a kowace rana musamman saboda satar mai da kuma barnatar da shi da ake yi.

Hako man fetur a arewacin Najeriya zai iya zama madogara don tara kudaden shiga ga kasar da kuma cike gibin da ake samu a kasafin kudi, in ji masana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.