Isa ga babban shafi

Najeriya: Gubar abinci ta kashe mutum 11 'yan gida daya a Benue

Wasu ‘yan gida daya sun 11 sun mutu sakamakon guba da suka ci a abinci a yankin Ikobi da ke karamar hukumar Apa ta jihar Benue.

Wani nau'i na abinci kenan
Wani nau'i na abinci kenan © South China Morning Post via Get - South China Morning Post
Talla

Mazauna kauyen sun ce ‘yan gida dayan sun mutu ne sakamakon zargin da ake cewa abincin da suka ci na dauke da sindaran kashe kwari da aka zuba wanda ya wuce kima

Daga cikin wadanda abin ya rutsa da su akwai: Adi Ale, Ochefije Ojo, Maria Ojo, Aipu Ochefije, Aboyi Ngbede Ochefije, Mary Ochoyoda, Ehi Abu, Blessing Abu, Peace Ochoyoda, Ojochono Daniel da kuma Favour Edoh.

Shida daga cikin wandanda suka mutu rahotanni sun tabbatar da cewa sun rasu ne a rana guda, inda sauran suka rasu bayan kwanaki biyu.

Farfesa Muhammad Adah, shine basaraken yankin na ikobi, ya kuma shaidawa jaridar dailytrust da ake wallafawa a kasar cewa, an samu irin wannan ibtila’I a watan satumba.

Ya ce shakkun gubar abinci ya karu ne yayin da biyar daga cikin wadanda abin ya shafa suka mutu a rana guda a kauyen, ya kara da cewa an gayyaci kwararru daga ma’aikatar lafiya ta jihar domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar.

Muhammad Adah ya ce har yanzu ana dakon sakamakon binciken mutuwar mutanen daga hukumomin da abun ya shafa.

An bayyana cewa, akwai wadanda kuma suka yi rashin lafiya bayan sun ci abincin, said ai sun samu sauki a halin yanzu, bayan sun samu kulawar gaggawa daga jami’an kiwon lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.