Isa ga babban shafi

An samu raguwar masu kamuwa da HIV AIDS a Najeriya- NACA

Hukumar da ke yaki da cutar Sida ko kuma AIDS a Najeriya NACA ta bayyana raguwar masu kamuwa da cutar HIV a sassan kasar idan an kwatanta da yadda kasar ke gani a shekarun baya.

Daga shekarar 2017 zuwa yanzu an samu raguwar masu kamuwa da cutar HIV AIDS a Najeriya.
Daga shekarar 2017 zuwa yanzu an samu raguwar masu kamuwa da cutar HIV AIDS a Najeriya. REUTERS/Mariana Bazo
Talla

Darakta Janar na hukumar ta NACA Gambo Aliyu da ya ke bayar da alkaluman cutar gaban taron manema labarai gabanin ranar yaki da cutar Sida ta duniya a ranar 1 ga watan Disamba, ya ce alkaluman masu kamuwa da cutar ya ragu daga mutum dubu 103 da 404 a shekarar 2019 zuwa mutum dubu 92 da 323 a shekarar 2021.

A cewar Gambo Aliyu, saukar alkaluman masu dauke da cutar ta HIV AIDS nan una cewa Najeriyar ka iya cimma kudirin Majalisar Dinkin Duniya game da rage masu kamuwa da cutar nan da shekarar 2030.

Shugaban hukumar ta NACA, ya ce la’akari da yadda ake samun damar gaggauta gwajin cutar a yanzu yana matukar taimakawa wajen dakile yada cutar da kuma tsanantarta zuwa AIDS.

Gambo Aliyu ya ce daga watan Satumban da ya gabata akalla mutane miliyan 1 da dubu dari 619 da 133 ne ke karbar kulawar cutar ta HIV lamarin da ke nuna karuwar masu samun kulawa idan an kwatanta da mutum dubu 838 da 020 wadanda ke karbar wannan kulawa a shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.