Isa ga babban shafi

Adeleke ya karbi ragamar mulkin Osun

Ranar Lahadi aka rantsar da Ademola Adeleke a matsayin sabon Gwamnan Jihar Osun, sakamakon nasarar da ya samu a zaben da akayi watannin da suka gabata.

Sanata Ademola Adeleke
Sanata Ademola Adeleke RFI hausa
Talla

Sabon gwamnan wanda nan take ya rufe asusun ajiyar jihar, ya bayyana aniyarsa ta bunkasa bangaren ilimi da tsaro da kula da lafiya da gina kayan more rayuwa, tare da sakin mara ga kananan hukumomi da kuma bangaren shari’a.

Adeleke ya kuma sanar da soke duk wasu nade naden da tsohon gwamnan yayi tun daga ranar 7 ga watan Yulin wannan shekara, cikinsu harda nada manyan sakatarorin gwamnati 30 da Oyetola yayi a makon jiya.

Sabon gwamnan ya kuma sauya sunan jihar daga ‘The State of Osun’ da ake kira, zuwa sunanta na assali, wato Jihar Osun.

Yayin bikin wanda ya samu halartar dan takarar shugaban kasar PDP Atiku Abukakar da gwamnonin jihohi da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, Gwamnan mai barin gado Adegboyega Oyetola yace ya barwa sabon gwamnan kundin da ya kai naira biliyan 14 a lalitar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.