Mazan Najeriya za su fara zaman jego don taya matansu reno
Gwamnatin Najeriiya ta amince a fara bai wa ma’aika maza hutun kwanaki 14 domin taya matansu da ke zaman-jego reno kamar yadda shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayyar kasar ta sanar.
Wallafawa ranar:
Shugabar ma’aikatan gwamnmatin Dr. Folashede Yemi Esan ta bayyana haka ne a ranar 25 ga wannan wata na Nuwamba a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa, babu namijin da za a ba shi irin wannan hutu fiye da sau daya cikin shekaru biyu, sannan kuma ga haihuwa hudu kacal.
Kazalika za a bada irin wannan hutun ga mutumin da ya dauko karamin yaron da bai wuce watanni hudu da haihuwa ba domin renon sa.
DR. Yemi t a ce, bayar zda irin wannan hutun na da aamuhimmaicni musamman don samar da kdangon kauna tsakanin jaariri ko jaririya ga iyaye maza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu