Isa ga babban shafi

Kotu ta yi umurnin a kamo babban hafsan sojin Najeriya

Kasa da mako guda bayan da wata kotu a Abujan Najeriya ta yanke  wa Sufeto Janar na 'yan sandan kasar Baba Alkali, hukuncin daurin watanni 3 a gidan yari, wata kotun ta daban a Minna dake Jihar Neja ta bada umurnin kamo mata shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahya da kuma tsare shi a gidan yari saboda kin mutunta umurninta. 

Manjo Janar Farouk Yahaya, baban hafsan sojin Najeriya.
Manjo Janar Farouk Yahaya, baban hafsan sojin Najeriya. © NIgerian Army
Talla

 

Mai shari’a Halima Abdulmalik ta bada wannan umurnin sakamakon korafin da aka gabatar a gabanta, yayin da ta kuma bada sammacin kamo mata kwamandan rundunar TRADOC dake Minna, Janar Olugbenga Olabanji saboda kin gabatar da kansa a kotun. 

Abdulmalik ta ce kotun ta bada umurnin kamo mata shugaban rundunar sojin da kwamandan TRADOC domin kaisu gidan yari saboda kin mutunta umurnin da ta bayara a ranar 12 ga watan Oktoba. 

Mai shari’ar tace bayan tsare su a gidan yarin, zasu ci gaba da zama har zuwa lokacin da zasu mutunta umurnin da ta gabatar baki daya. 

Wannan umurni na zuwa ne bayan makamancinsa da wata kotu ta daban ta bayar a Abuja akan shugaban Hukumar EFCC Abdurasheed Bawa, saboda kin mutunta umurnin kotu. 

Wadannan hukunce hukunce sun haifar da mahawara a Najeriya, ganin irin mutanen da abin ya shafa da kuma batun mutunta umurnin kotu a lokacin mulkin dimokiradiya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.