Isa ga babban shafi

Hukumar zabe ta roki 'yan Najeriya su taimaka wajen kare mata ofisoshi

Biyo bayan jerin hare hare a kan ofisoshin zabe a Najeriya, hukumar zaben kasar ta yinkira ga ‘yan Najeriya su kalli ofisoshinta matsayin kadarorin kasa, su kuma kare su gabanin zaben shekarar 2023.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya. AP
Talla

Shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahamood Yakubu ne ya mika wannan bukata a yayin wani taro da ya yi da kungiyar dattawar yammacin Afrika a shelk watar hukumar a Abuja.

Tsohon shugaban Sierra Leone, Ernest Bai Koroma daa kuma wani tsohuwar shugabar  Gambia, Fatoumata Jallow Tambajang ne suka jagoranci tawagar dattawan na yammacin nahiyar Afrika.

Yakubu ya ce akwai wasu ‘yan faannoni da suke ci wa hukumar tuwo a kwarya, babba daga cikinsu ita ce matsalaar rashin tsaro da ya addaabi kasar.

Ya ce a kasa da makonni 3, ofisoshinsu 3 ne aka kai wa hare hare a fadin kasar, lamarin da ya kai adadin ofisoshin da aka kai wa hare zuwa 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.