Isa ga babban shafi

Buhari yayi watsi da makiyayan Najeriya - Miyetti Allah

Kungiyar Fulani makiyaya dake Najeriya wadda ake kira Miyetti Allah ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da watsi da muradunsu, a daidai lokacin da ya taimakawa bangarorin ci gaba da dama, cikin su harda na manoma. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Sabon shugaban kungiyar Baba Usman Ngelzerma yace yayin da Buhari ya ware makudan kudade zuwa bangarorin noma da suka hada da manoman shinkafa da wasu nau’in abinci, babu wani shiri da gwamnatin kasar ta gabatar domin taimakawa makiyaya. 

Ngelzerma yace a cikin shekaru 8 da suka gabata, babu wani shirin inganta rayuwar makiyaya da gwamnati ta aiwatar da shi wadanda zasu taimakawa ‘yayan kungiyarsu wadanda ke ci gaba da fama da matsaloli musamman na ‘yan bindiga barayin shanu dake kashe ‘yayansu suna kwashe musu dukiyoyi. 

Shugaban kungiyar yace ganin irin tsangama da hare haren da ake kaiwa ‘yayan kungiyarsu, babu wadanda suka fi bukatar taimako da ya wuce su, amma kuma abin takaici shine har yanzu basu ga alamar samun tallafi daga bangaren gwamnati ba. 

Ngelzerma yace ta yaya za’a bar wannan sana’a da ta kunshi triliyoyin nairari a hannu mutanen da basu da ilimin zamani a kuma ce za’a samu ci gaba? 

Shugaban kungiyar wanda ya bayyana bangaren kiwo a matsayin wanda ke kusa da yadda man fetur ke samarwa Najeriya kudade, yace muddin aka inganta bangaren da kuma zamanantar da shi, ba karamar arziki kasar zata samu ba, yayin da dubban mutane kuma zasu samu ayyukan yi. 

Dangane da masu cewar kiwo sana’a ce wadda babu hannun gwamnati a ciki kuwa, Ngelzerma yace idan haka ne me yasa gwamnati take taimakawa kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.