Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya sun samu galabar murkushe Yan bindiga a Zamfara

Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta ta jiragen sama akan sansanin ‘yan bindigar Jihar Zamfara dake kauyen Mutumji a karamar hukumar Maru, abinda yayi sanadiyar kashe akalla 60 daga cikinsu. 

Misali na 'yan bindiga.
Misali na 'yan bindiga. © Daily Trust
Talla

Rahotanni sun ce daga cikin mutanen da harin ya ritsa da su harda mata da kuma yara wadanda suke yankin lokacin da harin ya ritsa da su. 

Bayanai sun ce harin ya biyo bayan koken da mazauna kauyukan Malele da Ruwan Tofa da 'yan awaki suka gabatar na cewar ‘yan bindigar sun farwa garuruwansu, abinda ya sa sojojin kai musu dauki ta sama. 

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da aukuwar lamarin, yayin da ya kuma bayyana mana cewar yayin kai daukin ta sama sojojin cikin kuskure sun hallaka wasu daga cikin abokan aikin su dake kai hari ta kasa. 

Majiyar tamu tace yayin da ake wannan, wasu yan bindigar sun yiwa tawagar sojoji kwantar bauna inda suka kaiwa motocinsu guda 3 hari a yankin. 

Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar munanan hare hare daga 'yan bindiga wadanda ke sanyawa garuruwa haraji domin hana kai musu hari. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.