Isa ga babban shafi

Jirgin ruwa dauke da mutane sama da 100 ya dare gida biyu a Kebbi

Mutane 10 sun rasa rayukansu a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeiya, bayan da wani jirgin ruwa dauke da mata da yara sama da 100 ya rabe zuwa gida biyu cikin wani kogi.

Wasu masu aikin ceto bayan kifewar jirgin ruwan da ya taso daga Neja zuwa jihar Kebbi a arewacin Najeriya a 2021.
Wasu masu aikin ceto bayan kifewar jirgin ruwan da ya taso daga Neja zuwa jihar Kebbi a arewacin Najeriya a 2021. © Daily Trust
Talla

Jirgin ruwan na dauke da fasinjoji ne da ke dawowa daga gona a kogin Neja, inda ya karye a daidai lokacin da ya tunkari kauyen Samanaji da ke gundumar Koko-Besse.

Jami’ai sun ce jirgin ya nutse bayan rabewar da ya yi ne, sakamakon yawan da fasinjoji suka yi masa fiye da kima.

Zuwa yanzu mutane 80 aka tabbatar da cewa an ceto daga hatsarin jirgin ruwan, yayin da tsamo gawarwaki 10, wasu 10 kuma suka bace, wadanda ake kyautata zaton cewa su ma sun mutu, saboda tsawon lokacin da suka shafe a karkashin ruwa ba tare da an samu nasarar tsamo su ba.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, shugaban karamar hukumar Koko-Besse, Yahaya Bello, ya ce lamarin ya faru da daren ranar Talata, lokacin da karamin kwale-kwalen ya dauki mutane sama da 100 cikinsu har da manoman shinkafa zuwa Samanaji.

Ya ce 80 daga cikin fasinjojin sun kubuta, inda aka samu gawar mutum 10 daga cikin su, yayin da ake ci gaban da neman sauran wadanda suka bace a ruwa, kuma ana ci gaba da binciken inda ruwa ya kai su.

Lodin fasinjoji fiye da kima, da kuma rashin kula na daga cikin manyan dalilan da suke janyo yawaitar nutsewar ruwa a Najeriya

A watan Mayu na shekarar 2021 kusan ’yan kasuwa 100 ne suka nutse a ruwa a lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a jihar Kebbi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.