Isa ga babban shafi

Na'ura za ta fara tona asirin direbobi masu shan giya a Najeriya

Ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO, ta kiyasta adadin mutane kusan dubu 50 suka rasa rayukansu a Najeriya a sanadiyyar haddura akan hanyoyin kasar, yayin da Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasar ta bullo da wani sabon shiri na amfani da wata na'ura da za a rika yi wa direbobi gwaji da ita don sanin ko sun sha barasa ko kuma a'a. 

Wani hatsarin mota
Wani hatsarin mota © africafeeds
Talla

Wannan adadi, ya wakilci kusan kashi 3 na daukacin alkaluman wadanda suka mutu ta wannan hanya a fadin duniya, kana Najeriya ce ta zamo ta 54 a yawan haddura a kan hanyoyi a duniya. 

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Ibrahim Malam Goje daga jihar Bauchi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.