Isa ga babban shafi

Za mu sa a kamo mana gwamnan CBN - Majalisar Wakilan Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi barazanar amfani da cikakken karfin doka wajen bayar da sammacin kama gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele da wasu mukarrabansa da suka yi watsi da gayyataar majalisar.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwill Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwill Emefiele © CBN
Talla

Shugaban Majalisar Wakilan, Femi Gbajabiamila ya bayyaana fushinsa kan yadda gwamnan babban bankin ya ki halartar zama tare da wani kwamitin wucen-gadi na majalisar karkashin jagorancin Alhassan Ado Doguwa.

A cikin wata wasika da Emefiele ya aike wa zauren majalisar a wannan Alhamis ya bayyana cewa, ba zai samu damar halartar zaman ba.

Majalisar Wakilan ta gayyace shi domin yi mata bayani game da gazawar bankin na CBN wajen wadata sassan Najeriya da sabbin takarddun kudin Naira a daidai lokacin da wa’adin ranar 31 ga watan nan na Janairiu na daina amfani da tsoffin kudin ya kusan cika.

Da dama daga cikin ‘yan Najeriya na farbagar halin da za su tsinci kansu a ciki muddin wa’adin daina amfani da tsoffin Naira ya kawo karshe ba tare da sauya musu da sabbin ba, lamarin da masana tattalin arziki ke cewa, zai jefa miliyoyin mutanen kasar cikin talauci.

Gwamnatin tarayya ta ce, ba za ta tsawaita wa'adin ba kamar yadda 'yan kasar suka bukata, yayin da 'yan kasuwa ke kokawa kan rashin musanya musu tsohuwar Nairar da sabuwa a bankunan kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.