Isa ga babban shafi

Gwamnan CBN ya roki 'yan Najeriya da su ci gaba da layi a banki

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su nuna fahimta tare da cewa takardun da aka sake fasalin za su rika yawo kuma za a iya samun su.Emefiele ya yi wannan roko ne a wani taron manema labarai a Legas na musamman kan sabbin kudaden.

Sabuwar takardar kudin Naira dubu 1 ta Najeriya.
Sabuwar takardar kudin Naira dubu 1 ta Najeriya. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Lura  da yada aka fuskanci tarzoma da zanga-zanga a wasu wuraren ganin wahalhalun da 'yan kasar ke fuskanta wajen samun sabbin takardun Gwamnan babban bankin Najeriya ya roki ‘yan kasar da su ci gaba da hakuri,inda ya karasa da cewa "Na fahimci tashin hankali kuma ina rokon ku da ku yiwa Allah, za a kawo karshen wannan al’almari.

Gwamnan babban bankin Najeriya ya bayyana cewa sun samu ganawa da shugabanin bankuna,an cimma fahimtar juna da nufin biyawa jama’a bukatun su cikin sauki.

Gwamnan babban bankin Najeriya ya dau alkawali tare da bayyana cewa za’a kawo karshen tsarin nan na takaita adadin kudin da ake iya cirewa, za a cire iyaka kuma mutane za su iya gudanar da harkokinsu na kasuwanci kamar yadda aka saba a baya,” in ji  Emefiele.

A kan cajin da wakilan da ke gudanar harakokin su a POS, ke yi kan duk wani ciniki da abokan cinikinsu, babban gwamnan bankin ya bukaci bankunan da su dakatar da cajin kan PoS.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.