Isa ga babban shafi

Farfesa Pate na Najeriya ya zama shugaban Gavi

Hukumar Gudanarwar ‘Gavi Alliance’ da ke samar da magungunan rigakafi ga kasashen duniya ta sanar da nada ‘dan Najeriya kuma tsohon Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate a matsayin sabon shugabanta. 

Farfesa Muhammad Ali Pate
Farfesa Muhammad Ali Pate © The Cable
Talla

Pate wanda kwararren likita ne da ya samu kwarewa a bangaren cututtuka masu yaduwa zai karbi ragamar jagorancin Gavi daga ranar 3 ga watan Agusta mai zuwa daga hannun Seth Berkley ‘dan Amurka wanda ke rike da mukamin tun daga shekarar 2011. 

Shugaban Hukumar Gudanarwar Gavi kuma tsohon shugaban Hukumar Gudanarwar Kungiyar Kasashen Turai, Jose Manuel Barroso ya bayyana Pate mai shekaru 50 a matsayin fitaccen masanin da ya shahara a duniya daga cikin wadanda suka nemi wannan mukamin, kuma aka ba shi saboda cancantarsa. 

Farfesa Ali Pate wanda ya fito daga Jihar Bauchi, ya rike mukamin Karamin Ministan Lafiya a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2013 lokacin da ya jagoranci farfado da shirin rigakafi da kuma samar da asibitocin kula da lafiya a yankunan kananan hukumomi tare da samar da sabbin magungunan rigakafi a Najeriya tare da kuma jagorancin yakin kawar da cutar polio. 

Pate ya kuma zama Daraktan Lafiya na Bankin Duniya da kuma Daraktan dake kula da Kudaden Bankin tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021, wanda ya kunshi sanya ido akan asusun yaki da cutar korona da dauke da Dala biliyan 18. 

Kafin wannan nadi, Farfesa Pate na aiki ne a matsayin shehun malami a Cibiyar Horar da Jagororin Kula da Lafiya ta Julio Frenk da ke makarantar Koyar da Jami’an Kiwon Lafiya ta Havard Chan, kuma ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan karramawar da Gavi ta masa wajen nada shi a matsayin shugaban daya daga cikin cibiyoyin da suka fi tasiri a harkar kula da lafiyar duniya. 

Ita dai wannan cibiya ta Gavi, wata kungiya ce mai zaman kanta da aka kirkiro a shekara ta 2000 domin samar da magungunan rigakafi ga kasashe masu tasowa. 

Tun lokacin da aka kirkiro ta, ta gabatar da magunguna ga yara sama da miliyan 981 da kuma kare yara miliyan 16 da dubu 200 daga mutuwa, baya ga rage yawan yaran da suke mutuwa a kasashe 73. 

Gavi na jagoranci wajen shirin tattara magungunan da manyan kasashe da kamfanoni ke bayarwa a matsayin gudumawa tare da Hukumar lafiya ta duniya da kuma kawancen kungiyoyin dake tinkarar  annoba. 

Shirin Gavi ya yi nasarar aikewa da maganin rigakafin cutar korona biliyan guda da miliyan 900 zuwa kasashe da yankuna 146 na duniya, da zummar ganin an taimakawa kasashe 92 da tattalin arzikin su bashi da karfi. 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.