Isa ga babban shafi

Buhari ya yi umarnin ci gaba da amfani da tsohuwar takardar Naira 200

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da ci gaba da amfani da tsohuwar takardar kudi ta Naira 200 har zuwa nan da ranar 10 ga watan Aprilu mai zuwa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Bayo Omoboriowo
Talla

A wani jawabinsa ga ‘yan kasar da safiyar yau Alhamis, Buhari ya ce za a ci gaba da amfani da tsohuwar Naira 200, yayinda babban bankin kasar zai ci gaba da karbar tsaffin kudin na 500 da 1000.

Shugaban dai bai sahale ci gaba da amfani da tsaffin kudin na 500 da 1000 ba duk da hukuncin kotun kolin kasar da ta yi umarnin ci gaba da amfani da takardar kudin har zuwa lokacin da za ta ci gaba da shari'a kan karar da aka shigar gabanta a ranar 22 ga watan da muke ciki na Fabarairu.

Matakin sauya takardar kudin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da al'ummar kasar ke shirin kada kuri'a a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan da muke.

Matakin jawabin ga kasa da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na zuwa ne bayan kiraye-kiraye baya ga korafe-korafen talakawa biyo bayan halin kuncin da jama'a suka shiga bayan sauya takardar kudin ta Naira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.