Isa ga babban shafi

'Yan takarar shugabancin Najeriya sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Masu neman kujerar shugabancin kasa a Najeriya, sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja, gabanin zaben kasar da zai gudana ranar Asabar mai zuwa.

Taron yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja
Taron yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja © dailytrust
Talla

Daga cikin wadanda suka halarci taron zaman lafiyar, akwai Omoyele Sowore na jam’iyyar AAC, Bola Tinubu daga APC da kuma Peter Obi na jam’iyyar LP.

Sauran sun hada da Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP, da kuma Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban Kenya Jomo Kenyata  da kuma tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki na daga cikin wadanda ssuka halarci taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.