Isa ga babban shafi

An kama mutumin da ya lashi takobin hana gudanar da zabe a Najeriya

Jami’an ‘yan sandan Finland sun cafke Simon Ekpa, wani mai rajin kafa kasar Biafra wanda kuma ya sha yin barazanar hana gudanar da zaben 2023 a Najeriya.

Simon Ekpa, wani da ya ayyana kansa a matsayin mai rajin kafa kasar Biafra daga Finland
Simon Ekpa, wani da ya ayyana kansa a matsayin mai rajin kafa kasar Biafra daga Finland © Cheer News
Talla

Ekpa ya jima yana furta kalaman tunzuri domin haddasa tashin hankali a Najeriya daga can mazauninsa a na kasar Finland.

Ekpa ya sha yin kira ga mutanen yankin kudu maso gabashin Najeriya da su rika mutunta umarnin Kungiyar IPOB na zaman gida kan tilas a kowanne mako, abin da ya kara fito da manufarsa ta neman raba kan Najeriya.

Kafin cafke shi a wannan Alhamis, gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata takardar korafi domin ganin an cafke mutumin da ke goyon bayan ballewar kabilar Igbo daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.