Isa ga babban shafi

Bankuna sun musanta shirin dakatar da ayyukansu saboda zabe

Kungiyar bankunan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa, babban bakin kasar CBN zai dakatar da ayyukansu tsawon kwanaki biyar har sai an gudanar da zaben shugaban kasa a ranar Asabar.

Dandazon 'yan Najeriya a gaban wani banki a kokarinsu na samun sabbin takardun Naira.
Dandazon 'yan Najeriya a gaban wani banki a kokarinsu na samun sabbin takardun Naira. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

An dai shafe kwanaki jita-jitar shirin dakatar da ayyukan ilahirin bakunan Najeriya na yawo a tsakanin ‘yan kasar, inda wasu majiyoyi ke cewa, matakin zai fara aiki ne daga ranar 23 zuwa 27 ga watan Fabarairun da muke.

Sai dai cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta Rasheed Bolarinwa, kungiyar bakunan Najeriya ta bayyana rahotannin a matsayin labaran karya.

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta fara kokarin aiwatar da shirin takaita amfani da tsabar kudade wajen hada-hada da kuma sauya fasalin takardun naira dubu 1 da 500 da kuma 200, tare da daina amfani da tsaffinsu, ‘yan Najeriya ke fuskantar matsalar hada-hadar kudade ta Intanet, watakila a dalilin nauyi fiye da kima da rumbun samar da karfin yanar gizon ke dauka.

A ranar Laraba Kotun Kolin Najeriya ta sake dage ranar da za ta yanke hukunci kan bukatar soke haramcin cigaba da amfani da tsaffin kudaden da aka sauyawa fasali, karar da gwamnonin jihohin Najeriya fiye da 10 suka shigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.