Isa ga babban shafi

Takaitaccen tarihin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour

Dan takarar neman kujerar shugabancin Najeriya na jam'iyyar Labour ko kuma LP, Peter Gregory Obi na daya daga cikin wadanda ake sawa ran samun gagarumar nasara a babban zaben kasar na karshen mako wanda ‘yan takara 18 za su fafata.

Peter Obi dan asalin jihar Anambra.
Peter Obi dan asalin jihar Anambra. AFP/Pius Utomi Ekpei
Talla

Peter Gregory Obi dan asalin jihar Anambra ta kudancin Najeriya an haifi shi ranar 19 ga watan Yulin shekarar 1961 a garin Onitsha inda ya fara karatun firamare da sakandire a makarantar Christ the king college da ke garin Onitsha, sannan a shekarar 1984 ya ci gaba da karatunsa a jami’ar Nsukka inda ya samu digirin farko a bangaren falsafa.

Bayan samun digirin farko Peter Obi ya kuma halarci kwalejin horar da kasuwanci a Lagos kana ya sake karanta kasuwanci a jami’ar Havard da Cambridge da kuma Oxford a birnin London da birnin New York. 

Peter Obi attajiri ne da ya shiga harkar siyasa a shekarar 2006, ya kuma zama gwamnan jihar ta Anambra, kana ya sake tsayawa takara a karo na 2 cikin shekarar 2010, inda ya doke abokin adawarsa karkashin jam’iyyar PDP Farfesa Charles Chukwuma Soludo da ya kasance tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, abinda ya ba shi damar cigaba da rike mukamin gwamnan jihar ta Anambra zuwa 2014. 

A shekarar 2019, Peter Obi ya tsaya takara a matsayin mataimakin Atiku Abubakar karkashin jam’iyyar PDP, zaben da Shugaba Mohammadu Buhari da ke jam’iyyar APC yayi nasarar lashewa. 

A cikin watan Maris din shekarar 2022 da ta gabata, Peter Obi ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben da ke tafe karkashin jam’iyyar PDP, daga bisani ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Labour bayan Atiku Abubakar ya ki daga masa kafa yayinda shi kuma ya ki yadda da sake takara a matsayin mataimaki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.