Isa ga babban shafi

Takaitaccen tarihin dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar NNPP

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Dr Rabi’u Musa Kwankwaso dan asalin jihar Kano ta arewacin Najeriya na sahun ‘yan takarar da ke da miliyoyin magoya baya a sassa daban-daban na kasar, inda ya rike mukamin Gwamna har sau biyu baya ga Sanata na tsawon wa’adi guda da kuma ministan tsaro a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaron Najeriya da ke neman kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar NNPP.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaron Najeriya da ke neman kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar NNPP. Premium Times
Talla

An haifi Dr Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar 21 ga watan Oktoban 1956 a garin Kwankwaso da ke karamar hukumar Madobi ta jihar Kano, ya kuma yi karatun firamare a garin na Kwankwaso baya ga Sakandire a Gwarzo kana ya je Kano Technical College gabanin samun karama da babbar diploma a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna yayinda a shekarar 1982 zuwa 1983 ya samu digiri a kwalejin Midddlesex kana digirin digir-gir a Jami’ar Loughborough cikin shekarar 1985 duk dai a Birtaniya yayinda ya samu PhD a jami’ar Sharda da ke India.

Kwankwaso mai shekaru 66 wanda ya ke da gogewa a fasahar ruwa ya yi aikin shekaru 17 karkashin ma’aikatar ruwa gabanin tsunduma harkokin siyasa a shekarar 1992, inda ya rike mukamin gwamnan Kano sai a shekarun 1999 zuwa 2003 kana 2011 zuwa 2015 yayinda ya rike mukamin Sanatan Kano ta tsakiya daga 2015 zuwa 2019.

Kwankwaso na da Mata guda Salamatu Kwankwaso da yara 6 ciki har da Mustapha Kwankwaso da kuma Al’amin baya ga Aisha Kwankwaso.

Kwankwaso ya rike mukamin ministan tsaron Najeriya daga shekarar 2003 zuwa 2007 karkashin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

A shekarar 2014 yayin zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC Kwankwaso ya zo na biyu kasa da Muhammadu Buhari da kuri’u 974 yayinda Atiku Abubakar ke biye da shi da kuri’u 954.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.