Isa ga babban shafi

Takaitatcen tarihin dan takarar jam'iyar PDP Atiku Abubakar

Alhaji Atiku Abubakar, dan siyasar Najeriya kuma dan kasuwa wanda ya taba zama mataimakin shugaban kasar daga shekarar 1999 zuwa 2007 a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo.

Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a Najriya karkashin jam'iyar PDP a zaben 2023
Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a Najriya karkashin jam'iyar PDP a zaben 2023 © REUTERS/Paul Carsten
Talla

Ya tsaya takarar gwamnan jihar Adamawa a shekarar 1990, 1996, daga baya, a shekarar 1998, aka zabe shi kafin ya zama mataimakin Olusegun Obasanjo a zaben shugaban kasa na 1999, da kuma 2003.

Atiku Abubakar ya yi takarar shugabancin Najeriya sau biyar bai yi nasara ba, wato a 1993, 2007, 2011, 2015, da 2019.

Ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar Social Democratic Party a shekarar 1993, inda ya sha kaye a hannun Moshood Abiola da Baba Gana Kingibe.

Ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Congress a 2007 inda ya zo na uku yayin da Muhammadu Buhari na ANPP ya kasance na biyu, a zaben da Umaru Yar’Adua na PDP ya lashe.

A shekarar 2011 ya sha kaye a hannun Goodluck Jonathan a zaben fitar da gwani karkashin jam’iyyar PDP da aka yi.

A shekarar 2014, ya koma jam’iyyar APC kafin zaben shugaban kasa na 2015 kuma ya fafata a zaben fidda gwani tare da shugaba mai ci Muhammadu Buhari.

A shekarar 2017, ya koma jam’iyyar PDP, kuma ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2019, inda ya sake shan kaye a hannun shugaba Muhammadu Buhari.

A watan Mayun 2022, aka zabe shi a matsayin wanda zai wakilci jam’iyyar PDP a zaben 2023 bayan ya doke Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas a zaben fidda gwani.

Kadan daga cikin tarihin Atiku Abubakar

An haifi Atiku Abubakar ne a ranar 25 ga watan Nuwamban shekarar 1946 a garin Jada, wani kauye wanda a wancan lokaci yake Kamarun a karkashin mulkin mallakar Burtaniya daga bisani yankin ya hade da Tarayyar Najeriya a zaben raba gardama na ‘yan kasar Kamaru a shekarar 1961.

Mahaifinsa ya yi adawa da ra'ayin ilimin boko, inda ya yi kokarin ya hana Atiku Abubakar shiga makarantar.

Lokacin da gwamnati ta gano cewa Atiku ba ya zuwa makarantar, mahaifinsa ya yi kwanaki a gidan yari har sai da mahaifiyar Aisha Kande ta biya tara.

Abubakar yana da shekaru takwas ya shiga makarantar firamare ta Jada dake Adamawa. Bayan kammala karatunsa na firamare a shekarar 1960, ya samu gurbin shiga makarantar sakandaren lardin Adamawa a wannan shekarar, tare da wasu dalibai 59. Ya kammala karatunsa na sakandare a shekarar 1965 bayan ya yi aji uku a jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka.

Bayan kammala karatunsa na Sakandare, Abubakar ya yi karatu na dan lokaci a Kwalejin 'yan sandan Najeriya da ke Kaduna. Ya bar Kwalejin ne a lokacin da ya kasa gabatar da sakamakon da ya samu a darasin lissafi, kuma ya yi aiki na dan lokaci a matsayin jami’in haraji a ma’aikatar kudi ta yankin, inda daga nan ya samu gurbin karatu a Makarantar nazarin Kiwon Lafiya ta Kano a shekarar 1966.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.