Isa ga babban shafi

'Yan sanda a Kano sun haramta gangamin Jam'iyyun APC, NNPP da PDP

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta bukaci dakatar da gangamin siyasar da jam’iyyun APC, NNPP da kuma PDP suka shirya gudanarwa yau alhamis a kwaryar birnin jihar sakamakon gaza shawo kansu don ganin wasu daga ciki sun janyewa wasu da nufin kaucewa samun rikici tsakanin magoya baya.

Wasu magoya bayan jam'iyyun siyasa a jihar Kano ta Najeriya.
Wasu magoya bayan jam'iyyun siyasa a jihar Kano ta Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Dukkanin jam’iyyun 3 da ake adawa da juna sun tsara gudanar da gangamin yau lamarin da ya sanya fargabar iya samun rikici lura da yadda dukkaninsu su ke shirin kai ziyara yanki guda.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta jihar Kano ta fitar ta bakin kakakinta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Muhammadu Yakubu ya yi iyakar kokarinsa wajen shawo kan jam’iyyun 3 a ganawar da ya yi da su don gani wasu sun barwa wasu gangamin na yau amma dukkaninsu suka cije.

A cewar Abdullahi Kiyawa wannan cijewa da jam’iyyun 3 suka yi ne ya tilasta kwamishinan daukar matakin dakatar da dukkanin gangamin na su har zuwa bayan zaben shugaban kasa.

Jam’iyyun 3 da suka kunshi APC mai mulki da NNPP karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso kuma dan takarar shugaban kasa kana PDP su ke matsayin manyan abokanan adawa kuma masu rinjayen magoya baya a jihar ta Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.