Isa ga babban shafi

Jonathan ya roki 'yan Najeriya su ba da hadin kai don gudanar da sahihin zabe

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya roki jama’ar kasar da su bada gudumawa wajen gudanar da zaben shugaban kasa gobe asabar cikin kwanciyar hankali. 

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Wata sanarwar da Jonathan ya gabatarwa manema labarai ta bayyana bukatarsa ta ganin masu kada kuri’u sun yi amfani da damar da su ke da ita wajen zaben shugabannin da su ke so ba tare da fargaba ba. 

Tsohon shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya da su tinkari zaben da muhimmanci, sadaukarwa da kuma kishin kasa da zai ba su damar kada kuri’a cikin lumana ba tare da zub da jini ba. 

Jonathan ya kuma janyo hankalin hukumar zabe da jami’an tsaro da kuma duk masu ruwa da tsaki akan shirin zabe, cikin su har da kungiyoyin fararen hula da su gudanar da aikin su da gaskiya da kuma amana, inda ya ke cewa ta wannan hanyar ce kawai jama’ar kasar za su samu kwarin gwuiwar ci gaba da mutunta tsarin dimokiradiyya. 

Ga ‘yan siyasa kuwa, Jonathan ya janyo hankalin su domin fahimtar cewar amana ce suke bukata daga hannun jama’a domin yi musu aiki, saboda haka kuskure ne su dinga tilasta kansu wajen ganin sun ci zabe ta kowacce hanya. 

Tsohon shugaban ya kuma janyo hankalin matasa domin fahimtar cewar sune manyan gobe, saboda haka ya zama wajibi su kaucewa bada damar amfani da su wajen tada hankali. 

Jonathan yace kuskure yadda wasu mutane suka mayar da tashin hankali ya zama abin ado lokacin zabe, inda ya bukace su da su fahimci muhimmancin dimokiradiya wadda ta zama hanyar zaben shugabannin da suke so cikin kwanciyar hankali. 

Tsohon shugaban ya bayyana cewar yana da muhimmanci ‘yan Najeriya su kare wannan dimokiradiyar da aka kwashe sama da shekaru 20 ana amfani da ita wajen zabo shugabanni na gari. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.