Isa ga babban shafi

An fara kidayar kuri'u a sassan Najeriya

An fara kidayar kuri'u a zaben Najeriya da aka gudanar a ranar Asabar mai cike da cece-kuce, inda manyan 'yan takara hudu ke fafutukar gudanar da mulkin dimokuradiyya a kasar da ke da mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, bayan da aka samu jinkiri da tashe-tashen hankula.

Masu diba sunayen masu zabe a Najeriya
Masu diba sunayen masu zabe a Najeriya © Akintunde Akinleye/Reuters
Talla

Kusan mutane miliyan 90 ne suka cancanci kada kuri’a domin zaben shugaban kasar da zai maye gurbin Muhammadu Buhari, inda ‘yan Najeriya da dama ke fatan sabon shugabansu zai magance matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da kuma rage karuwar talauci.

A karon farko tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999, an samu manyan ‘yan takara da suka fito don kalubalantar jam’iyyun APC da PDP.

A Legas da sauran garuruw,n jama’a da dama ne suka taru domin kallon kidayar kuri’u a rumfunan zabe, inda aka kirga kuri’u da hannu kafin a aika da su zuwa ga hukumar INEC.

Zabubbukan da suka gabata a Najeriya sau da yawa sun fuskanci magudi. Dan takarar PDP Abubakar ya yi ikirarin cewa an tafka magudi a lokacin da Buhari ya doke shi a zaben 2019 kafin kotun koli ta yi watsi da karar da ya shigar.

Har yanzu INEC ba ta bayyana lokacin da za a bayyana sakamakon zaben a hukumance ba duk da cewa ana sa ran nan da kwanaki masu zuwa za a san makomar kasar.

Duk wanda ya ci zaben shugabancin Najeriya zai fuskanci kalubalen da suka dabaibaye tattalin arzikin kasar mafi girma a Afirka, da ke fama da matsaloli masu sarkakiya, tun daga ayyukan ta’addanci da ‘yan bindiga da ‘yan aware zuwa hauhawar farashin kayayyaki da kuma karuwar talauci.

Buhari, wanda tsohon kwamandan soji ne, zai sauka daga mulki bayan wa'adi biyu, inda masu suka suka ce bai cika alkawuran da ya dauka na tabbatar da tsaron Najeriya ba.

Karancin takardun kudi

Karancin man fetur da kuma kudaden da aka samu sakamakon musayar takardun kudi na banki a daidai lokacin zaben ya kuma jefa ‘yan Najeriya da dama cikin cikin mawuyacin hali, inda kasar ta fuskanci hauhawar farashin kayayyaki sama da kashi 20 cikin 100.

Domin samun nasarar zama shugaban kasa dole ne dan takara ya samu kuri'u mafi yawa, amma kuma ya samu kashi 25 cikin 100 na jihohi 36 na Najeriya.

Zagaye na biyu

Idan babu dan takara da ya yi nasara, za a gudanar da zagaye na biyu a cikin kwanaki 21 tsakanin 'yan takara biyu, sakamakon da ba a taba ganin irinsa ba wanda wasu manazarta ke cewa mai yiyuwa ne a wannan karon.

Bayanai sun yi nuni da cewa kasar kusan ta rabu tsakanin arewa da ke da yawan musulmi da kuma kudu masu rinjaye na kirista, kuma tana da manyan kabilu uku a fadin yankuna: Wato Yarbawa a kudu maso yamma, Hausa/Fulani a arewa da kuma kabilar Igbo a kudu maso gabas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.