Isa ga babban shafi

Boko Haram sun tarwatsa masu zabe a jihar Bornon Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kai samame karamar hukumar Goza dake jihar Borno. dai dai lokacin da masu zabe ke shirin kada kuri’a a zaben shugaban kassa da na ‘yan majalisun tarayya a Najeriya.

Wasu daga cikin tawagar mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin tawagar mayakan Boko Haram AFP
Talla

Sarkin Goza, Muhammad Shehu wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce mutum biyar ne suka samu munanan raunuka yayin harin.

“Boko Haram  sun kaddamar da hare-hare a tsakiyar garin Goza, inda suka rika harbin kan mai ‘uwa dawabi. Mutum biyar sun samu raunuka, kuma tuni aka mika su babban asbitin birnin Maiduguri,” in ji sarki Shehu.

Bayanai sun ce mayakan sun is garin da misalin karfe 8:30 na ssafe, daidai lokacin da ake kokarin fara tantance masu zabe. Mutane da dama da suka tsere sun kasa komawa rumfunan zabe, yayin da ake ta kokarin shawo kan wasu, amma abin ya ci tura.

A cewar sarkin, jami’an tsaro sun samu nasarar korar mayakan.

Goza dai na daga cikin yankin da fitaccen dan siyasar nan, Sanata Ali Ndume, ke wakilta a zauren majalisar dattijan Najeriyar, wanda ke neman komawa kujerar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.