Isa ga babban shafi

APC ta lashe zakamakon zaben Ekiti yayin da PDP ta lashe na Osun

Jam’iyya mai mulkin Najeriya ta APC, wadda ke marawa Bola Tinubu baya ta lashe zaben jihar Ekiti da yawan kuri’u 201,494, sai Atiku Abubakar na PDP da ya samu yawan kuri’u 89,554, inda jam’iyyar Labour ta Peter Obi ta zo na uku da kuri’u 11,397, yayin da NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ta samu kuri’u 264.

Atiku da Tinubu
Atiku da Tinubu © Guardians
Talla

Haka zalika, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Osun.

Atiku ya samu nasara a kananan hukumomi 20 da jimillar kuri’u 354,366 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 343,945 kuma ya samu nasara a kananan hukumomi 10.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya zo na uku a zaben da jimillar kuri’u 23,283, sai Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 713.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.