Isa ga babban shafi

Ko wane ne zai gaji shugaba Muhammadu Buhari?

Yayin da ‘yan Najeriya ke dakon sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi jiya a fadin kasar, ‘yan takara 18 ke jiran tsammani domin sanin wanda zai samu galaba a tsakaninsu domin karbar rantsuwa ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa. 

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari © lailasnews
Talla

A karon farko tun daga shekarar 2003, wannan shekarar ce kawai shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke shirin barin karagar mulki ba ya takarar wannan zabe saboda kawo karshen wa’adinsa na shekaru 8 kamar yadda dokar kasa ta tanada. 

Buhari ya fara takarar neman shugabancin Najeriya ne a shekarar 2003 a karkashin Jam’iyyar ANPP, inda ya fafata da shugaban wancan lokaci Olusegun Obasanjo lokacin da yake neman wa’adi na biyu, kuma Obasanjon ya samu nasara. 

A shekarar 2007, Buhari ya kara da Malam Umaru Musa Yar’adua na jam’iiyyar PDP, inda a karon farko aka samu ‘yan takara biyu daga jiha guda suna fafatawa domin neman shugabancin Najeriya, kuma a karshe ‘Yar Adua ya samu nasara. 

A shekarar 2011, Buhari ya sake takara a karkashin sabuwar jam’iyyarsa ta CPC amma shugaba Goodluck Jonathan wanda ya gaji kujerar 'Yar Adua ya kada shi. 

A shekarar 2015 bayan an yi hadin gambiza, wato Jam’iyyun ANPP da CPC da kuma AC sun hade, sun tsayar da Buhari a matsayin dan takara, abin da ya ba shi nasara kayar da shugaba mai ci Goodluck Jonathan. 

A shekarar 2019, Buhari ya sake takarar wa’adi na biyu inda ya samu nasarar kayar da Atiku Abubakar domin yin wa’adi na biyu. 

Bayan kwashe shekaru 20, a wannan shekara ta 2023 ne kawai Buhari ba ya takara, kuma bayan kada kuri’arsa ta karshe a matsayin shugaban kasa, shugaban ya ce ya gamsu yadda aka inganta harkokin zaben Najeriya musamman wajen amfani da na’urorin zamani ta yadda magudin zabe yanzu ke da matukar wahala. 

Buhari ya dade yana shaida wa kasashen duniya cewar aniyarsa ita ce ganin an inganta zabe ta hanyar da za a rika bai wa jama’a abin da suka zaba, maimakon sauya alkaluma wajen gabatar musu da shugabannin da ba su ci zabe ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.