Isa ga babban shafi

An saye kuri'un 'yan Zaria da shinkafa

Wasu ‘yan siyasa a garin Zaria da ke jihar Kaduna ta Najeriya sun bi mutane gida-gida suna rarraba musu shinkafa domin sayen kuri’unsu a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a jiya Asabar .

Wasu masu kada kuri'a a zaben Najeriya.
Wasu masu kada kuri'a a zaben Najeriya. © rfi hausa
Talla

Kazalika ‘yan siyasar sun karbi lambobin asusun mutanen, inda suka yi musu alkawarin tura musu kudi muddin suka zabi jam’iyyarsu.

Daya daga cikin mutanen da suka sayar da kuri’unsu da shinkafar ya tabbatar wa RFI Hausa cewa, ‘yan siysar sun rarraba duk mutun uku buhun shinkafa guda.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren bayanin da ya yi mana.

Wasu rahotannin da muka samu na cewa, akwai dimbin mutanen karkara da su ma suka sayar da kuri'unsu da awara a yankin arewacin Najeriya.

Wannan na zuwa ne duk da kokarin da wasu kungiyoyi da malaman addinai suka yi wajen fadakar da jama'a domin kauce wa sayar da kuri'unsu da wani abin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.