Isa ga babban shafi

Jam'iyyar ADC ta nesan ta kanta daga kiran soke zaben Najeriya

Jam’iyyar adawa ta ADC a Najeriya, ta barranta kanta daga kiraye-kirayen da wasu jam’iyyun hamayya suka yi na a sake sabon zaben shugabancin kasar.

Shugaban Hukumar INEC da wasu jami'ansa a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaben 2023.
Shugaban Hukumar INEC da wasu jami'ansa a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaben 2023. AP - Ben Curtis
Talla

A ranar Talatar nan ne, babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da kuma jam’iyyar Labour suka fitar da sanarwar bukatar hakan, tare da neman shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da ya sauka daga mukaminsa.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da jam’iyyun suka gudanar a Abuja, babban birnin kasar, sun yi zargin cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da ya gudana a sassan kasar.

Julius Abure, shugaban jam’iyyar Labour, wanda kuma yayi magana a madadin sauran jam’iyyun adawar, ya ce sashe na 60, karamin sashe na 5 na dokar zabe, ya ce dole ne baturen zabe idan zai gabatar da sakamakon kuri’un da aka kada, sai ya bayyana adadin wadanda aka tantance, da kuma adadin wadanda suka kada kuri’a a rubuce, kamar yadda INEC ta tabbatar.

Ya kara da cewa an gaza bin matakan hukumar zabe wajen bin ka’idojin da aka gindaya domin kuwa ya kamata a shigar da dukkanin sakamako a na’urar IReV, kafin a sanar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.