Isa ga babban shafi

Bola Tinubu ya karbi takardar shaidar lashe zabe daga INEC

Zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya karbi takardar shaidar lashe zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC.

Zabebben shugaban kasar Najeriya Alhaji Bola Ahmed Tinubu da mai dakinsa Oluremi Tinubu a lokacin karbar shaidar nasarar zabe a hannun shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmud Yakubu.1 ga watan Maris 2023
Zabebben shugaban kasar Najeriya Alhaji Bola Ahmed Tinubu da mai dakinsa Oluremi Tinubu a lokacin karbar shaidar nasarar zabe a hannun shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmud Yakubu.1 ga watan Maris 2023 © RFI
Talla

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmaud Yakubu ne ya mika takardar ga sabon zababben shugaban da mataimakinsa Kashim Shettima.

Yayin jawabin da ya gabatar a taron, Tinubu ya roki 'yan Najeriya musamman magoya bayan jam'iyyun adawa da su bashi hadin kai wajen samar da ci gaba ga Najeriya, ba tare da la'akari da banbancin ra'ayi ba.

Sabon zababben shugaban ya kuma ce kofarsa a bude take, ga duk wanda zai kawo shawarar da za ta taimaka wajen fitar da kasar daga cikin kangin da take ciki.

A cikin jawabin nasa, mai cike da sakonni, Bola Ahmed Tinubu yana mai fatan ganin nan gaba an dama da matasa da mata a fannoni daban-daban, wajen gina sabuwar Najeriya, ta yadda za ta yi gogayya da wasu manyan kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.