Isa ga babban shafi

Kotu ta aike da Alhassan Ado Doguwa gidan yari

Rundunar 'yan sandan jihar Kano, ta gurfanar da Al-Hassan Ado Doguwa, dan majalisar da ke wakiltar Doguwa/Tudun Wada a zauren majalisar wakilai, sakamakon zargin sa da hannu a kisan wadanda ba su ji ba basu gani ba, a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gudana.

Alhassan Ado Doguwa
Alhassan Ado Doguwa © RFI
Talla

An cafke Doguwa ne a ranar Talata, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja, daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutum uku ne suka mutu nan take, a lokacin da aka kaddamar da harin.

Kotun da aka gurfanar da dan majalisar ta aike da shi gidan yari, tare da dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar bakwai ga watan Maris.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kano, Sp Abdullahi Kiyawa, ya ce sun cafke dan majalisar ne, bayan ya ki amsa gayyatar jami'an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.