Isa ga babban shafi

Amurka ta bukaci INEC ta magance matsalar na'urori kafin zaben gwamnoni

Amurka ta yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, INEC da ta magance matsalolin fasaha da ake zargin sun na’urar BVAS gabanin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a yi ranar 11 ga watan Maris.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Ned Price, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, a cikin wata sanarwa, ya ce ‘yan Nijeriya suna da hakkin a magance musu wannan matsalar, la’akari da yadda suka yi kyakkyawan fata a zaben shugaban kasa da aka kammala.

“Mun bi sahun masu sanya idanu na kassa da kasa wajen yin kira ga INEC da ta yi dub ana tsanaki tare da gyara kura-kuran da suka faru, kafin zaben 11 ga watan Maris.

“Mun fahimci cewa da dama daga cikin al’ummar Najeriya da sauran jam’iyyun siyasa sun bayyana rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa, musamman yadda aka yi amdani da wwasu sabbin na’urori da a karshe basu gamsar ba,” in ji Price.

Price, ya kuma shawarci sauran ‘yan takarar da suka sha kaye, da su yi amfani da bangaren shari’a wajen kwato hakkokinsu, ba wai amfani da hanyar da bata kamata ba.

Amurka ta kuma yabawa kungiyoyin fararen hula da kuma kafofin yada labarai, bisa irin rawar da suka taka wajen wayar da kan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.