Isa ga babban shafi

EU ta nesanta kanta daga batun soke zaben Najeriya

Kungiyar Kasashen Turai ta EU ta nesanta kanta daga rahotannin dake cewa ta bukaci sauke shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu daga kujerarsa. 

Tutar kungiyar tarayyar Turai
Tutar kungiyar tarayyar Turai © REUTERS / YVES HERMAN
Talla

 

Wata sanarwar da kungiyar ta rabawa manema labarai tace wancan sanarwar labarin kanzon kurege wanda bai fito daga wurinta ba, saboda haka babu hannunta a ciki. 

Mai Magana da yawun kungiyar a Abuja, Agnes Doka tace babu hannun ta a cikin sanarwar da kungiyar NDI ta Amurka ta gabatar wanda ake zargin cewar ta sanya hannu a ciki. 

Kungiyoyin da suka sanya ido a zaben Najeriya da dama sun bayyana samun wasu kura kurai, musamman na rashin sanya sakamakon zaben daga mazabu a rumbunan ajiyar hukumar zabe, yayin da suka yabawa ‘yan Najeriya saboda fitowar da suka yi da kuma yin zaben cikin kwanciyar hankali. 

Tuni biyu daga cikin manyan ‘Yan takaran zaben Atiku Abubakar da Peter Obi suka ce zasu je kotu domin kalubalantar sakamakon zaben. 

Obi yace babu tantama shi ya lashe zaben, kuma yana da hujjojin da zai gabatarwa kotu, yayin da Atiku yace wannan shine zabe mafi muni a tarihin dimokiradiyar Najeriya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.