Isa ga babban shafi

Gobarar bututun mai ta kashe sama da mutum 10 a Jihar Ribas

Akalla mutane 12 ne aka tabbatar sun mutu, sakamakon fashewar bututun mai da aka dasa ba bisa doka ba a jihar Ribas, dake Kudu maso kudancin Najeriya.

Ana fargabar adadin mamatan ka iya zarta 12
Ana fargabar adadin mamatan ka iya zarta 12 AP - Ramon Espinosa
Talla

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a a yankin Rumuekpe, a cikin karamar hukumar Emaukacin hukuma ta jihar.

Kakakin 'yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ya ce har yanzu ba a tantance mutanen da suka mutu ba.

Sai dai binciken jami’an tsaro ya gano cewa, mutanen da suka mutu, lamarin ya rutsa da su ne lokacin da ssuke kokarin satar mai.

Motoci biyar ne da kuma babura masu kafa uku (Wato Keke NAPEP) guda hudu ne suka kone kurmus.

Satar danyen mai da kuma bude haramtattun matatun mai sun zama ruwa dare a yankin Niger Delta, duk da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na magance matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.