Isa ga babban shafi

Shugaban Najeriya Buhari zai halarci taron MDD a Qatar

A Asabar din nan shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari  ya yi balaguro zuwa birnin Doha don halartar taron kasashe 5 da suka fi koma bayan tattalin arziki.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022 © Nigerian Presidency
Talla

Babban mai bai wa shugaban na Najeriya shawara a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya ce ziyarar ta  biyo bayan gayyatar da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani yaw a shugaban Najeriya ce.

Ya ce wadanda suka yi wannan balaguro tare da shugaban Najeriya sun hada da manyan jami’aan gwamnati, wadanda ake sa ran za su sanya hannu a kunshin yarjeniyoyi da za a kulla da gwamnatin Qatar.

Kakakin  shugaban na Najeriya ya ce za a fara taron ne daga ranar 5 zuwa 9 ga watan Maris din nan, kuma an saba yin sa ne a kowane bayan shekaru 10.

Ya kara da cewa a birnin Doha, shugaba Buhari zai karfafa kudirin Najeriya na taimaka wa kasashe marasa galihu wajen tinkarar kalubalen da ke tarnaki gaa ci gabansu.

Ana sa ran shugaba Buhari ya koma Najeriya a r,anar   8 gawatan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.