Isa ga babban shafi

INEC na son kotu ta sauya izinin da ta bai wa Atiku da Obi

Hukumar Zaben Najeriya, INEC ta bukaci kotun da ke sauraren korafin zaben shugaban kasa da ta sauya izinin da aka bai wa Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour na nazartar kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben shugaban kasa na 2023.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu tare da jami'ansa a yayin alkalancin zaben shugaban kasa na 2023.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu tare da jami'ansa a yayin alkalancin zaben shugaban kasa na 2023. AP - Ben Curtis
Talla

A wani kudiri  da ta fitar a ranar 4 ga wannan wata na  Maris, INEC ta yi fatan kotun za ta sauya umarnin wucen-gadi da ke hana ta taba kayayyakin zaben, tana mai cewa, akwai bukatar ta sake seta na’urar BVAS domin gudanar da zaben gwamnonin johohin Najeriya a wannan Asabar mai zuwa.

A ranar 3 ga watan nan ne, kotun daukaka karar ta bai wa Atiku Abubakar da Peter Obi damar nazartar na’urar ta BVAS da INEC ta yi amfani da ita a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan jiya.

Kotun ta hana INEC ta’ammuli da na’urar har sai ‘yan takarar biyu sun gudanar da binciken kwa-kwaf a cikin na’urar biyo bayan zargin da suka yi na yi musu magudi a zaben.

‘Yan takarar biyu,  sun shigar da kara ne bayan sun fadi zaben, inda suka sha kashi a hannun Bola Ahmed Tinubu da INEC ta ayyaa shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Yanzu haka INEC ta ce, lallai akwai bukatar da tura kwararrun injiniyoyinta akan lokaci domin fara seta na’urar  karkashin shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnoni, tana mai cewa, in ba haka ba, to akwai yiwuwar dage zaben na gwamnoni kamar yadda wata majiya ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.