Jagororin PDP na gudanar da zanga-zanga a Abuja
A Najeriya, jam’iyyar adawa ta PDP na gudanar da zanga-zanga a babban birnin Tarayyar Abuja don nuna rashin amincewa da yadda aka gudanar da babban zaben kasar.
Wallafawa ranar:
Jagororin jam’iyyar, a wani mataki na nuna goyon baya, sun hade da sauran kusoshin jam’iyyar ciki har da kwamitin amintattu na kungiyar wadanda suka fito wannan zanga zangar.
Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar, Atiku Abubakar, da shugaban jam’iyyar Dokta Iyorchia Ayu da daraktan yakin neman zaben jam’iyyar, gwamna Aminu Waziri Tambuwal na daga cikin masu ruwa da tsaki na PDP da suka fito gangamin a ofishin hukumar zaben kasar.
Baya ga nuna rashin amincewa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar, jam’iyyar PDP na jayayya da yadda hukumar zaben kasar ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
Tun da farko PDP ta bukaci a soke zaben shugaban kasar, a kuma gudanar sabo, sakamakon abin da ta kira kurakurai da aka samu a wasu sassan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu