Isa ga babban shafi

NNPP ta zargi Ganduje da sakin fursunoni don haddasa fitinar zabe

Gwamnan Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya yi afuwa ga fursunoni 12 a aka yanke musu hukuncin kisa, yayin da ya sauya wa wasu fursunoni 6 hukuncin kisa zuwa na daurin rai-da-rai, amma jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar ta yi zargin cewa, an yi wa fursunonin afuwa ne domin su samu damar shiga cikin ‘yan dabar da za su haddasa rikici a zaben da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganguje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganguje © This Day
Talla

Jam'iyyar ta NNPP ta yi wannan zargin ne a cikin  wata budaddiyar wasika da ta aika wa shugaban kasar Muhammadu Buhari gabanin zaben na gwamna da ‘yan majalisar jiha.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Gyaran Hali, SC Misbahu Lawan Nasarawa ya fitar ta ce, gwamnan ya kuma yi afuwa ga wasu mata hudu da aka yanke musu zaman gidan kaso na tsawon lokaci sakamakon kyawawan dabi’un da suke nunawa a yanzu.

Kazalika gwamna Ganduje ya bai wa kowanne fursuna kyautar Naira dubu 5 domin samun kudin komawa gida cikin iyalansa.

An gargadi fursunonin da aka yi wa afuwar da su zama nagartattu bayan sun koma cikn al’umma domin ci gaba da rayuwa.

Tuni bangaren gwamnatin jihar ta Kano ya musanta sakin fursuonin da zummar haddasa hatsaniya a yayin zaben mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.