Isa ga babban shafi

Kungiyoyin arewacin Najeriya sun bukaci a hukunta masu laifi lokacin zabe

Gamayyar kungiyoyin kishin al'umma na jihohin arewacin Najeriya 19 sun bukaci hukumomin kasar su hukunta wadanda aka samu da laifukan zabe, domin ya zama darasi ga masu yi wa dimukutadiyyar kasar makarkashiya.

Taron gamayyar kungiyoyin kishin al'ummar arewacin Najeriya
Taron gamayyar kungiyoyin kishin al'ummar arewacin Najeriya © Abubakar Abdulkadir Dangambo
Talla

Kungiyoyin sun kuma ce Hukumar Zaben Kasar ta gaza samar wa al'ummar kasar abin da suka yi tsammani a babban zaben kasar na 25 ga watan jiya.

Jagoran gamayyar kungiyoyin kwamared Ibrahim Waiya ya ce duk da alkawuran da Hukumar Zaben kasar INEC, ba ta shirya gudanar da sahihin zabe ba.

Yace al'ummar kasar da farko sun yi ammanna cewar, INEC ta shirya wa zaben, har fiye miliyan 85 suka yi rajista,  amma sai ga shi an samu manyan kura-kurai da suka kashe gwiwar mutane da dama.

Kazalika, kungiyoyin sun yi Allah-wadai da tarzomar zabe da aka samu a wasu sassan kasar, Inda suka jaddada bukatar a hukunta duk wanda aka samu da hannu komai girman mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.