Isa ga babban shafi

Rikicin makiyaya da manoma ya haddasa asarar rayuka a Benue

Mutane da dama ne suka mutu a kauyuka daban-daban na karamar hukumar Kwande ta jihar Benue da ke arewa maso tsaiyar Najeriya, bayan da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hare–hare  a yankin.

Wasu Fulani makiyaya a Najeriya
Wasu Fulani makiyaya a Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Rahotanni sun ce har yanzu akwai mutane da dama sun ba ce, wasu kuma sun samu raunuka na harbin bindiga, sannan kuma an kona gidaje da dama kurmus.

Wani mazaunin yankin ya ce a cikin mako  da ya gabata ne aka fara kai wadannan hare-hare, wadanda suka bazu zuwa wasu wasu yankunan karamar hukumar Kwande ciki har da Moon da Mbaikyor da Mbadura da Ilyav.

Amma kungiyar makiyaya ta Mikyetti Allah ta ce akwai rikici da aka yi kwanan tsakanin makiyaya da mazauna kauyukan jihar  a kan kwace dabbobi.

kungiyar ta ce a yayin rikicin an kashe makiya, amma yanzu al'amura sun dai-dai ta bayan shiga tsakani da jami'an sojoji da kuma na sauran hukumomin tsaro suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.