Isa ga babban shafi

OIC ta taya Tinubu murnar lashe zaben Najeriya

Kungiyar Hadin-Kan Kasasshen Musulmi ta OIC, ta taya Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabairun da ya gabata.

Zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. © AP - Ben Curtis
Talla

Sakatare Janar na Kungiyar Mista Hissein Brahim Taha, shi ne ya mika sakon taya murnar ga Tinubu a cikin wata sanarwa da Darektan Yada Labarai na kungiyar, Mista Wajdi Sindi ya sanya wa hannu a birnin Jeddah na kasar Saudiya.

Babban Sakataren ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya sun daura wa zababben shugaban kasar nauyi saboda amannar da suka yi da manufofinsa wadanda suka samo asali daga dimbin basirarsa da kwarewarsa.

Mista Taha ya kuma tabbatar wa zababben shugaban cewa, kungiyar ta OIC za ta ci gaba da inganta huldar da ke tsakaninta da Najeriya  musamman ta fuskar bunkasa tattalin arzikin da zamantakewa da kuma yakar ta’addanci da tsattsauriyar akida.

Daga karshe, Babban Sakataren ya yi wa Tinubu fatan cimma nasara, yayin da ya yi wa daukacin al’ummar Najeriya fatan hadin-kai da samun ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.