Isa ga babban shafi

Hadin gwiwar kwararru ya samar da sabon nau'in gidan sauro a Najeriya

Wata tawagar kwararru daga jami’ar Jihar Kaduna da aka fi sani da KASU, ta samu nasarar kirkirar sabon nau’in gidan sauro a matsayin gudunmawa ga kokarin da ake yi na kawo karshen zazzabin cizon Sauron da ya addabi mutane.

Najeriya na dauke kwatankwacin kashi 31 cikin 100 na adadin mutanen da zazzabin cizon sauro  ya kashe a fadin duniya cikin shekarar 2021.
Najeriya na dauke kwatankwacin kashi 31 cikin 100 na adadin mutanen da zazzabin cizon sauro ya kashe a fadin duniya cikin shekarar 2021. REUTERS - EDGAR SU
Talla

Jami’in da ke hulda da jama’a na jami’ar ta KASU, Adamu Bargo ne ya bayyana nasarar da kwararrun suka yi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin nan.

Tawagar kwararrun ta gudanar da aikinta ne a karkashin jagorancin Farfesa Zakari Ladan na tsangayar ilimin sarrafa sinadarai a jami’ar jihar ta Kaduna, wanda yayi aiki tare da Dakta Mthunzi Fanyana na jami’ar Vaal daga kasar Afirka ta Kudu, sai kuma Dakta Bamidele Okoli na jami’ar Bingham da ke jihar Nasarawa a Najeriya.

Bayanai sun ce, namijin kokarin masanan da ya kunshi nazari da kuma samar da gidan sauron ya lakume naira miliyan 27, kudaden da aka samar daga gidauniyar bunkasa cibiyoyin bincke da nazarin kimiyya na NRF, wanda yake karkashin asusun bunkasa ilimin manyan makarantun Najeriya na TETFund.

Zazzabin cizon sauro ya dade yana halaka rayukan miliyoyin mutane a fadin duniya, musamman a kasashe masu tasowa ciki kuwa har da Najeriya.

Wata  kididdiga da aka fitar ta nuna cewar, ‘yan Najeriya akalla dubu 191,890 suka rasa rayukansu a dalilin zazzabin cizon sauro a shekarar 2021, kwatankwacin kashi 31 cikin 100 na adadin mutanen da suka mutu a fadin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.