Isa ga babban shafi

'Yan takara sama da 800 ne ke fafatawa a zaben gwamnoni a jihohi 28 na Najeriya

Yayin da ake gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jahohi a wannan Asabar din a Najeriya, ‘yan takarar kujerar gwamna 837 ne za su fafata a zaben da za’a gudanar a jahohi 28 daga cikin 36, sannan akwai ‘yan takara dubu 10 da 240 da zasu fafata wajen neman lashe kujerun ‘yan majalisar dokoki 993 a mazabu dubu 1 da 21 da ake da su a fadin kasar.

Hukumar zaben Najeriya ta ce ta shirya tsaf don gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majaloisun dokoki.
Hukumar zaben Najeriya ta ce ta shirya tsaf don gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majaloisun dokoki. AP - Sunday Alamba
Talla

Daga cikin jihohi 28 da za’a gudanar da zaben gwamnoni, 17 sun kammala wa’adin su na biyu, a jihohi irin su Taraba da Benue da Enugu da Ebonyi da Abia da Cross River da Delta da Akwa Ibom da Rivers da Kebbi da Sokoto da Kaduna da Katsina da Kano da Jigawa da Filato da kuma Neja, yayin da a ragowar jihohi 11 da suka hada da Lagos da Ogun da Oyo da Kwara da Zamfara da Gombe da Nasarawa da Yobe da Borno da Adamawa da kuma Bauchi gwamnonin ke neman tazarce.

A cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC, jihohi 8 da ba za’a gudanar da zaben gwamnoni a cikin su ba sun hada da Anambra da Bayelsa da Edo da Ekiti da Imo da Kogi da Ondo da kuma Osun.

Toh sai dai gabanin isowar ranar zaben, an samu rahotannin rikice-rikece musamman a jihohin da gwamnoninsu ke neman zarcewa.

Zaben gwamna a jihohin Kaduna da Filato da kuma Taraba na daukar hankali ta yadda wasu magoya bayan ‘yan takara ke amfani da kalaman nuna banbancin addini wajen sukar juna.

A jihohin Lagos da Zamfara da Oyo da Ogun da Bauchi da kuma Nasarawa, gwamnoninsu na fustantar babbar barazana daga bangaren ‘yan adawa wadanda ke neman raba su da kujerunsu.

Jihar Kano, wacce ake kallo a matsayin cibiyar siyasar arewacin Najeriya, jam’iyar APC da ke mulkin ta ne ke fuskantar babbar barazana daga bangaren jam’iyar NNPP ganin yadda ta lashe kujerun sanatoci biyu daga cikin uku da ake da su a jihar, tare da majalisar tarayyar 17 daga cikin 24.

A jihar Adamawa kuwa, gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ne ke fuskantar barazana daga Aishatu Dahiru Ahmed ‘yar takarar jam’iyar APC, inda wasu ke ganin watakila lokaci yayi da burin mata na zama gwamna a kasar zai cika a wannan karon.  

Domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’umma gabani, lokaci da kuma bayan zaben, tuni jami’an tsaron kasar suka kasance cikin shirin ko-ta-kwana don magance duk wani kalubale da zai taso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.